kididdiga

Ken Saro-Wiwa jr, mai shekara 47 wanda ɗa ne ga mai rajin Kare Mahallin nan na yankin Naija Delta a Najeriya, Ken Saro-Wiwa, ya mutu, a London.Gwamnatin tsohon shugaban mulkin sojan Najeriya, Janar Sani Abacha ce dai ta kashe Mahaifin Ken Saro-Wiwa jr, wato Ken Saro-Wiwa sr.Al'amarin kisan nasa wanda ya janyo kace-nace a fadin duniya, ya haddasa korar Najeriya daga Kungiyar Kasashe Rainon Burtaniya.Shi dai Saro-Wiwa ya jagoranci Kungiyar Cigaban Al'ummar Yankin Ogoni da aka fi sani da Mosop, a inda ya zargi kamfanin mai na Shell da lalata musu mahalli.

I BUILT MY SITE FOR FREE USING