tambaya ta biyu

Meye hukuncin saki lokacin jinin haila

01/08/2016
 

Tambaya ta 3

Meye maganin Hepatitis B

02/10/2016
 

tambaya ta 4

MAGANIN MATSALAR RASHIN BARCI TAMBAYA TA 2004 ********************* Assalamu alaikum malam don Allah MALAM inason ataimakamini inada matsala na rashin barci kusa da shekara daya da rabi kuma nayi ta zuwa asibiti amma dai matsalar bata gushe ba sannan BP dina 130/80.sannan shekara na 26 kuma banda qiba don haka ina son Dan Allah ataimaka mini .wassalamu alaikum.Daga Zayyanu A.Bala Dugu shanga LGA Kebbi AMSA ******* Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Wannan rashin barcin naka dole ya bama Likitocin zamani mamaki. Tunda gashi bugun zuciyarka normal, Kuma baka da hawan jini kp kuma sauran matsalolin dake haifar da rashin barci abisa fahimtar Likitocin Zamani. Ni shawarwarin da zan baka anan guda uku ne kamar haka: 1. Kaje wajen Qwararru wadanda suka san harkar Riqyah kayi musu bayani, ayi maka ruqyah irin ta Shafar Shaitanun Aljanu, da ku. A ruqyah domin magance sihiri ko kambun ido. 2. Ka koma zuwa ga Allah ta hanyar kokarin gyara zuciyarka da tunaninka. Ka tsarkake kanka ta hanyar yawaita tuba zuwa ga Allah da kuma nisantar manyan Kaba'irori. Ka kyautata dukkan dabi'unka da Mu'amalolinka. Kuma ka yawaita sauraron Wa'azuzzuka da karatun Alqur'ani da kuma zama tare da Salihan Bayin Allah. 3. Kada harshenka ya gushe daga ambaton Allah (zikirin Allah) da addu'o'i ako yaushe. Ba sai safe da yamma kawai ba. Kuma ka yawaita Salatin Annabi (saww) da karatun Alqur'ani. Da tsaiwar dare. 4. Shawara ta Qarshe kuma, ka nemi furen Albabunaj ko ganyensa ka rika dafa cokali biyu acikin ruwa kofi guda. Idan ya bararraka sai ka tace, ka sanya Sugar ko Zuma sannan kasha. Shi Albabunaj yana sassauta jijiyoyin dake cikin kwakwalwa, Yana hutasar dasu, Kuma yana Qara ma kwakwalwa samun nutsuwa. Don haka idan kasha zaka samu barci sosai da izinin Allah. ALLAH YA SAWWAKE.

03/14/2016

ko shan ruwan sanyi yanada illa ga lafiyar dan adam

Illar shan ruwan sanyi

10/19/2016
I BUILT MY SITE FOR FREE USING