
Uwar Gidan Shugaban Kasa, Hajiya Ai’sha Buhari ta nuna damuwa kan rikita-rikitar da ta dabaibaye babbar jam’iyyar APC da ke mulkin kasa. Inda a tattaunawa da Sashen Hausa na gidan Rediyon BBC, wanda aka fara gabatarwa a ranar Talata, Ai’sha Buhari ta bayyana cewa, “wannan lamarin yana damunmu matuka, saboda da yawa suna ganin su ne suka wahala, suka kafa gwamnati, amma kuma ba su cikin mulki a yau. Da yawa wadanda ba su gudanar da kowane irin abin kirki ba, wadanda ko katin jefa kuri’a ba su da shi, amma su ne ke tafiyar da komai a gwamnatin.”
A wani bangare na tattaunawar, Uwar gidan Shugaban Kasar ta kara da cewa, “abin da nake fargaba shi ne, tawayen mutane milyan 15 da suka kai Buhari saman gadon mulki.”
A yayin da aka tambayeta, ko Shugaban Kasa ya san abubuwan da ke kawo matsala a gwamnatinsa, Ai’sha Buhari ta bayyana cewa, “ko ya sani ko bai sani ba, wadanda suka zabe shi sun sani. Babu wani abu da zan gaya masa domin yana ganin komai.”
Ta ce, “dukkanin wadannan mutanen da ya sanya a gwamnatinsa, idan aka tambaye shi a cikin mutane 50, bai san mutane 45 ba. Ni kaina ban san su ba, duk kuwa da zamana da shi tsawon shekaru 25.”
A tambayar ko Buhari zai sake tsayawa takarar Shugabancin kasa a 2019 kuwa, sai ta amsa da cewa, ba ta da masaniya a kai, amma a kashin kanta ta cimma matsayarta kan hakan.
Cikakkiyar tattaunawar, wacce BBC Hausa za su sanya a ranar Jumr’ar nan da kuma gobe Asabar, sun nuna bukatar sake lale tun gabanin al’ummar kasa su yi wa Buhari tawaye.
Masu fashin bakin lamurran siyasa dai na ganin kalaman Ai’sha Buhari na nufin kwatankwacin maigidanta ya yi amfani da ‘yan siyasa ne wajen samun nasara, amma daga baya ya yi watsi da su, yanzu kuma ya gano kuskuren da ya yi yana son ya yi gyara a kai.