Assalamu Alaikum Malam Allah yaima sakayya da mafificin Alkairin duniya da lahira Ameen. Mal. Tambaya ta shine naje asibiti anyi min test ba tare da wani Abu Yana damuna ba. Sai akace Ina (hepatitis b) Kuma yanzu Ina Kan Shan magani Kuma sunce wai baa warkewa. Kuma nasan cewa babu wata cuta da Allah halitta ba magani. Mal dan Allah taimaka min. Allah nake roqo ya qarawa rayuwar malam da ta iyalinsa Albarka. NagodeAMSA*******Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.Nonon rakumi da kuma fitsarinsa suna daga cikin abinda ke magance matsalolin ciwon Hepatitis B in Allah yaso.Bayan haka kuma ka samu Man Habbatus Sauda cokali 1, Man Tafarnuwa cokali guda, Ka zubasu acikin ruwan dumi rabin kofi. Sannan ka sanya ruwan Khal cokali guda. Ruwan zuma shi kuma cokali uku.Ka gaurayasu ka shanye. Zaka ci gaba da yin haka har tsawon kwanaki sittin (60).In sha Allah zaka samu waraka da yardar Allah. Babu kokonto.Hakanan zaka iya hada :- garin Habbatus sauda cokali goma.- Garin Yansun cikali 5.- Garin Kirfa cokali 7.- Garin ganyen Mangoro cokali 5.- Garin ganyen Lemon tsami cokali 3.- Garin citta cokali 3.- Garin kanumfari cokali 2.- Garin Zogale cokali 3.Ka zubasu acikin zuma ka gauraya ka ajiye. Kullum zaka rika zuba cokali 3 acikin ruwan shayin Na'a-Na'a Kana sha. Zaka maimaita safe da yamma kullum. Har zuwa kwana 60.Allah ya sawwake. Allah yasa adace.