HUKUNCIN SAKIN AURE ALOKACIN JININ HAILATAMBAYA TA 2006********************Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu. Malam ina da tambaya ne.Dama shekaru kusan 2 na taba yi maka tambaya a fb kan matsalar aurena, bana samun kwanciyar hankali musamman ta wurin rayuwar aure, nayi kokarin naga ya gyara amma abun ya gagara, to a karshe dai na nemi ya sakeni kuma ya sakenin.. to malam anan ina da laifi agun Allah da na nemi sakin??Sai tambayata ta 2 yaya hukuncin yin saki a cikin haila? naji wasu malaman na cewa sakin bai yiwu ba, to malam yaya abun yake? Allah sakawa malam da AlkhairiAMSA*******Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.Hakika shi yin aure Sunnah ne bisa dokokin addinin Musulunci. Amma yin adalci ga Matar da mutum yake aure shi kuma Farilla ne.Wannan adalcin ya hada da adalci wajen ciyarwa da shayarwa da suturtawa da muhalli da Sauran mu'amaloli na yau da kullum. Sannan kuma wajibi ne Namiji ya zamanto yana da cikakkiyar lafiyar da zai iya biya ma matarsa bukatarta ta sha'awar Jima'i.Amma idan ya zamanto Mace ta nemi sawwakewa daga wajen Mijinta saboda abinda take gani na rashin adalci acikin zamantakewar auren, to babu wani laifi akanta.Amma idan ya zamanto komai yana tafiya daidai, amma duk da haka ita ta nemi rabuwa da Mijinta, to anan akwai laifi akanta. Kuma Mijin yana da damar ya saketa ko kuma yayi mata Khul'i. Wato yace ta mayar masa da sadakin da zai isheshi ya auri wata matar irinta.AMSAR TAMBAYARKI TA BIYU: Magana mafi inganci kuma mafi rinjaye ita ce Duk wanda ya saki matarsa acikin lokacin da take jinin haila, to hakika ya aikata bidi'ah amma sakin nasa ya yiwu.Hujjah anan ita ce hadisi na 4954 acikin SAHIHUL BUKHARIY. An karbo hadisin daga Anas bn Sirin yace Sayyiduna Abdullahi bn Umar (rta) ya bashi labari cewa "Ya saki Matarsa alokacin da take yin jinin haila. Don haka sai Sayyiduna Umar (rta) yaje ya tambayi Manzon Allah (saww) dangane da hukuncin wannan sakin. Sai Manzon Allah (saww) yace masa "KAJE KA MAYAR DA ITA".Anas bn Sirin yace "Na tambayeshi "Shin an kirga da wannan sakin?" sai yace mun "EH KWARAI KUWA".Hakanan Sa'eed bn Jubayr (ra) ya ruwaito daga Sayyiduna Abdullahi bn Umar (rta) yana cewa "Sakin Mace yayin da take cikin jinin Haila, ana kirgashi amatsayin saki ne. Awajena".Al Imam Dara-Qutnee acikkin tasa ruwayar yace "Sayyiduna Umar bn Khattab (ra) ya tambayi Manzon Allah (saww) akan hukuncin irin wannan sakin. Sai Manzon Allah (saww) yace masa "EH".(Aduba Fat-hul Baaree juzu'i na 9.shafi na 438.).Duk cikin Maluman Mazhabobin Musulunci babu wadanda suka ce wai in anyi saki acikin Haila bai yiwu ba. In banda IBNU TAIMIYYAH da IBNU HAZMIN da wasu 'yan Qalilan daga Almajiransu.Amma dai Mafiya rinjayen Sahabban Annabi (saww) da Tabi'ai da Tabi'ut Tabi'eena, da Maluman Mazhabobin nan hudu, duk Fatawarsu akan wannan Mas'alar shine "DUK WANDA YA SAKI MATARSA ACIKIN JININ HAILA, TO LALLAI YA AIKATA KUSKURE BABBA. AMMA MATARSA TA SAKU".Acikin FAT'HUL BAAREE juzu'i na tara, shafi na 438, Al Hafiz Ibnu Hajr Al-Asqalaniy yace Masu cewa irin wannan sakin bai yiwu ba, basu da wata Hujjah mai Qarfi. Kuma asalin irin wannan ra'ayin nasu sun samoshi ne daga KHAWARIJAWA DA MU'UTAZILAWA.Amma ga wadansu wuraren da za'a iya lekawa domin samun Qarin haske akan wannan Mas'alar :- HASHIYATUD DASUQIY juzu'i na 2 shafi na 570.- ALMUGHNIY na Ibnu Qudaamah juzu'i na 8 shafi na 237.- ALHIDAYAH (Na Mazhabin Hanafiyyah) juzu'i na 2 shafi na 357.WALLAHU A'ALAM.

I BUILT MY SITE FOR FREE USING