31 Dec
31Dec

An Mika Wa Buhari Tutar Shekau Da Al-Qur'ani Da Aka Gano A Dajin Sambisa

Shugaban rundunar Soja na 'Zaman Lafiya Dole', Manjo Janar Lurky Irabor ya mika wa Shugaba Muhammad Buhari ainihin Al-Qurani da tutar da Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau ke amfani da su wadda aka gano a Dajin Sambisa bayan fatattakan mayakan kungiyar da sojoji suka yi.

Sai dai, a yayin karbar tutar wanda aka gudanar a wurin liyafar da rundunar tsaron Fadar Shugaban kasa ta shirya a Abuja, Shugaba Buhari bai ce Uffan ba game da ikirarin Shekau na cewa har yanzu kungiyar na da tasiri a dajin Sambisa.

Comments
* The email will not be published on the website.
I BUILT MY SITE FOR FREE USING